Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya nakalto Khadin Zade yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa, hukumar tana kokarin takurawa kasar Iran a kan shirinta na makamashin Nukliya a yayinda wasu kasashen yamma, kamar Amurka, Faransa da Burtaniya suna kara bunkasa makamansu na nukliya, ba tare da kaji wata magana daga hukumar ba.
A baya bayan nan dai hukumar tana maganar cewa, wai mai yuwa sai an yi amfani da karfin soje wajen magance matsalar shirin nukliyar kasar Iran.
An cimma yarjejeniya tsakanin kasashen 5+1 da kuma Iran dangane da shirinta na makamashin Nukliya wanda ake kira JCPOA a takaice a shekara ta 2015, amma a shekara ta 2018 Amurka ta fice daga yarjejeniyar sannan ta kakabawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar.
A karshen shekarar da ta gabata ce aka fara tattaunawa don dagewa Iran takunkuman da kuma dawo da Amurka cikin yarjejeniyar, Sai dai har yanzun Iran tana jiran shawara ta karshe daga kasashen yamma, musamman A murka danagne da tattaunawar ta Vienna.
342/